DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Friday, October 9, 2026
HomeBabban Labari Kashim Shettima amintaccen abokin aiki ne - Tinubu

Kashim Shettima amintaccen abokin aiki ne – Tinubu

Shugaban Nijeriya, Bola Tinubu, da Uwargidansa, Oluremi Tinubu, sun taya mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, murnar cika shekaru 60, inda suka bayyana shi a matsayin ɗan kishin ƙasa, amintaccen abokin aiki kuma jajirtaccen ma’aikacin gwamnati.

A cikin saƙon taya murnar da Tinubu ya fitar a ranar Talata, ya ce yana taya Shettima murnar wannan babban matsayi na rayuwa tare da matarsa Nana, ’ya’yansa, iyalansa da abokan siyasarsa.

Jaridar Punch ta ruwaito Tinubu ya bayyana Shettima a matsayin mutum da rayuwarsa ta kasance mai cike da hidima, sadaukarwa da jajircewa wajen yi wa al’umma aiki. Ya ce amintaccen abokin aiki ne kuma ɗan kishin ƙasa da ya sadaukar da kansa ga abubuwan da suka dace.

Shugaban ƙasar ya kuma yaba da tarihin Shettima a harkar banki, da kuma gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban jihar Borno da Nijeriya, musamman a lokacin da ya kasance gwamnan jihar da kuma daga baya mataimakin shugaban kasa.

Ya ce Shettima ya nuna ƙarfin hali, jajircewa, tausayi da ƙwazo wajen inganta rayuwar jama’a a dukkanin mukaman da ya riƙe.

Tinubu ya kuma yaba da amincin Shettima ga jam’iyyar APC da kuma irin goyon bayan da yake bai wa gwamnatinsa wajen aiwatar da manufofin ‘Renewed Hope’ na gwamnatin Tinubu.

Shugaban ƙasar ya ce jagorancin Shettima na majalisar tattalin arziki ta kasa ya taimaka wajen daidaita manufofin tattalin arziki da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi.

Ya ƙara da cewa mutunta kundin tsarin mulki, cibiyoyin dimokuraɗiyya da kuma yin amfani da tattaunawa da shawarwari da Shettima ke yi, na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen ƙarfafa kyakkyawan shugabanci a ƙasar.

Tinubu ya ce amincin Shettima, hikimarsa da sanin ya kamata sun kasance muhimman ginshiƙai ga gwamnatinsa, yana mai gode masa bisa goyon baya da haɗin gwiwar da yake bayarwa wajen cika alkawuran Renewed Hope ga ’yan Nijeriya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata