DCL Hausa Radio
f DCL HAUSA FACEBOOK
Wednesday, October 14, 2026
HomeNishadiKashim Shettima ya bukaci ’yan fim da mawakan Arewa su goyi bayan...

Kashim Shettima ya bukaci ’yan fim da mawakan Arewa su goyi bayan Tinubu a 2027

Mataimakin shugaban Nijeriya Kashim Shettima, ya yi kira ga masu wasan kwaikwayo da mawaka daga Arewa da su mara wa shugaba Bola Ahmed Tinubu baya domin sake zaɓensa, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen tabbatar da haɗin kan Nijeriya.

Shettima ya ce Tinubu ya cancanci goyon bayan Arewa, tare da bayyana cewa gwamnatin tarayya za ta ci gaba da tallafa wa harkar nishaɗi da masu fasaha a yankin, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne ranar Laraba yayin da ya karɓi wata tawaga ta ’yan wasan kwaikwayo da mawaka daga Arewa, ƙarƙashin ƙungiyar Triple-R For Renewed Hope, a ofishin yaƙin neman zaɓen APC da ke Abuja.

Ya ce Arewa na da damar cin gajiyar shirye-shiryen gwamnatin Tinubu da suka shafi bunƙasa tattalin arziki, kirkire-kirkire, kare al’adu da samar da guraben ayyukan yi ga matasa.

Shettima ya kuma tabbatar wa tawagar cewa gwamnati za ta ci gaba da samar da shirye-shirye na musamman domin tallafa wa ’yan fim da mawaƙa a yankin Arewa.

Ya bukaci ƙungiyar da sauran masu ruwa da tsaki a Arewa su ci gaba da mara wa gwamnatin Tinubu da jam’iyyar APC baya, yana mai cewa amfanin manufofin gwamnati zai ci gaba da bayyana a fannoni daban-daban.

A nasa jawabin, Darakta-Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, Sanata Abdulaziz Yari, ya ce sake zaɓen Tinubu zai dogara ne kan hujjoji da ayyukan da gwamnatin ta aiwatar, inda ya bukaci ƙungiyoyin tallafa wa Tinubu da sauran mutane su duba ayyukan gwamnatin kafin yanke matsaya.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments

Mustapha madu bande on Tarihin marigayi Aminu Dantata