Home Sabon Labari Kasuwar ‘Gwari’ a Kaduna ta zama rusasshiya, kokarin Elrufai na zamanantar da...

Kasuwar ‘Gwari’ a Kaduna ta zama rusasshiya, kokarin Elrufai na zamanantar da kasuwanni

138
0

Yan kasuwa a wata kasuwa da ake kira da kasuwar ‘Gwari’ da ke kusa da Faskari Road a cikin garin Kaduna sun shaida wani abu da wasu ke ganin kamar almara, inda rahotanni ke cewa gwamnati ta rusa kasuwar gabadaya. A yanzu hotunan da ke yawo a shafukan sada zumunta na nuna yadda a ka dagargaza gine-gine da rumfuna a kasuwar.

Yadda kasuwar ta koma bayan an kammala rusata

Jaridar DCL Hausa ta tuntubi wani makwabcin kasuwar, wanda ya tabbatar da sahihancin hotunan da ake yadawa. Ya ce “ Wannan Dai Kasuwar Gwarin Unguwan Mu Da Ka Sani, Ita Fa. Gaskiya Ba Musan Abun Da Gwannati Take Cewa A Kan Wannan Lamarin Ba, Kawai Dai A Kawo Musu Notice, Lokaci Na Cika A Ka Zu A Ka Rusa.”

Kasuwar Gwari dai karamar kasuwa ce kuma daruruwan kananan ‘yan kasuwa ne ke sayar da abubuwa irinsu kayan miya da teloli da ke sana’ar dinki da masu sayar da abinci da sauran kananan sana’o’i. Babu shakka acewar wanda DCL Hausa ta tuntuba jama’ar da aka rushewa shagunan suna cikin zulumi. Akasarin ‘yan kasuwar sun dogara ga irin ribar da suke samu a kowace rana don ciyar da iyalansu. Yanzu abin zullumin shi ne sana’ar da za su iya samu a kankanin lokaci wace za ta iya rike musu iyalansu da biyan bukatun yau da kulum, “babu shakka jama’a na cikin jimami” acewar wani wanda ya ziyarci kasuwar bayan da aka rusata.

Wani matashi ke nan ke shawagi a kasuwar Gwari da mahukumtan jihar Kaduna suka rusa

Gwamna Nasiru Elrufa’i na jihar Kaduna ya yi kaurin suna wurin yin rusau a mukaman da ya rike a gwamnati. Har yanzu jama’an da gwamnan ya rusawa gidaje da shaguna a Babban Birnin Tarayyar Nijeriya Abuja, ba su manta da irin kuncin da suka shiga ba a lokacin da yake a matsayin Ministan Abuja. Amma kuma abin da kowa ba zai manta da shi ba, shi ne yadda har gobe ake yaba masa a kan yadda ya gyara garin Abuja; ya kawata birnin har ya zama abin kwatance a nahiyar Afirka.

Jama’a na cikin zulumi, ‘yan kasuwa sun yi jungum-jungum

A jihar Kaduna tun a zangonsa na farko, Gwamna Elrufa’I ya fara nuna bukatar rusa wasu kasuwannin jihar don ya sabuntasu, ya mayar da su na zamani tare da gina wasu sabbi da kuma gina manyan shaguna na alfarma da akafi sani da ‘shopping malls’. To amma ‘yan kasuwar sun nuna bijirewarsu. Kamar ya hakura bayan da ya sake lashe zaben gwamna a karo na biyu Elrufa’I ya sake dawo da kudurinsa na daukaka darajar kasuwanni da sake musu fasali ta hanyar fara rusa wasu kasuwanni a garin Zaria da cikin garin Kaduna.

Sai dai kawo yanzu babu wata sanarwa daga gwamnatin jihar Kaduna a kan wannan kasuwar Gwari da aka rusa a baya-bayan nan. A yanzu jama’a za su zura ido su ga ko gwamnati za ta sakewa kasuwar fasali ne kamar yadda ta ke kudurin yi wa Kasuwar Bacci da Central Market ko kuma za ta sauya kasuwar matsugunni.

 

Shin ya kuke kallon wannan yunkuri na kawo ci gaba?

 

 

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply