Home Labarai Katsina: APC ta dakatar da Sabo Musa

Katsina: APC ta dakatar da Sabo Musa

81
0

Jamiyyar APC reshen wakilin Kudu 3 a cikin karamar hukumar Katsina ta sanar da dakatar da Alh. Sabo Musa Hassan SSA Restoration na gwamnan jihar Katsina daga jamiyyar.

A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban jamiyyar na rikon kwarya reshen Wakilin Kudu III Tasi’u Dankasuwa tace an dakatar da Sabo Musa ne saboda rashin amsa gayyatar da jamiyyar ta yi masa.

Takardar tace dakatarwar ta fara Aiki daga Talatar nan 02/02/2021.

Hakan dai bai rasa nasaba da wani taro da Alh. Sabo Musa ya jagoranta wanda ya gudana a jihar Kano bisa zargin kafa wata tafiya mai suna “APC Pressure Group”.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply