Gwamnan jihar Katsina ya amince da sake nada Alhaji Murtala Ibrahim Kafur a matsayin mataimaki na musamman akan sadarwa ta gidajen rediyo (S.A Radio).
Bacin Alhaji Murtala Ibrahim akwai Hassan Usman Datti wanda shi kuma aka nada shi a matsayin S.A Media (1).
Rahotanni dai sun ce bayan wadannan nade-nade akwai karin wasu mutum takwas da su ma suka samu takardar tabbatar musu da mukami a gwamnatin Aminu Bello Masari.
Za mu kawo muku cikakken sunayensu da zarar suka zo hannunmu.
