Home Tsaro Katsina: An gano dabbobin sata sama da 33,000

Katsina: An gano dabbobin sata sama da 33,000

112
0

Kwamitin da gwamnatin jihar Katsina ta kafa don shiga tsakanin makiyaya da manoma ya samu nasarar karbowa tare da gano dabbobi sama da dubu talatin da uku.

Shugaban kwamitin Alh Abdul’aziz Lawal Kofar Sauri, ya shaidawa jaridar DCL Hausa cewa dabbobin sun hada da shanu, awaki, tumaki da jakuna a sassa daban-daban na jihar Katsina da ma makwabta.

Ya ce ya zuwa yanzu kwamitin ya kuma yi nasarar hannanta dabbobi sama da dubu talatin da daya ga masu su na ainihi, ta hanyar tantancewa tare da gabatar da takardar shaidar mallaka daga Hakimi ko Dagaci.

A shekarar 2016 ne dai gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Aminu Masari, ta kafa wannan kwamitin, da zummar karbowa tare da hannanta dabbobin da suka daidaice ta dalilin rikicin makiyaya da manoma.

 

Daga: Abdullahi Garba Jani, Katsina

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply