Home Coronavirus Katsina: An sallami wadanda gwamnati ta kebe saboda coronavirus

Katsina: An sallami wadanda gwamnati ta kebe saboda coronavirus

89
0

An sallami wasu mutane su hudu da ake tsammanin sun yi hulda da marigayi Dakta Aliyu Yakubu, likitan da ya rasu ta dalilin Corona a garin Daura jihar Katsina bayan da aka auna su cewa ba su kamu da cutar ba.

Gwamnati ta sallame su bayan sun cika wa’adin da aka diba ana kebe su daga jama’a don gudun kada sun kamu, kuma su yada wa wasu. A karshe kuma labari mai dadi ya zo cewa bama su kamu da cutar ba.

Tun bayan da gwamnati ta gano corona ce ta yi ajalin Dakta Aliyu ta kebe mutane da dama inda ta samu iyalansa da wannan ciwo kuma yanzu haka suna ci gaba da karbar magani.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply