Mutane shida daga cikin mutane goma sha hudu da aka killace a asibitin kwararri da ke Katsina sun warke daga cutar coronavirus har ma an sallame su.
Babban Likitan Asibitin Dr Bello Sulaiman Muhammad, ne ya sanar da hakan a Katsina, inda ya ce mutanen sun kwashe kwanaki 19 suna amsar kulawar likitoci.
Daga cikin wadanda suka warke din, kamar yadda babban likitan asibitin ya ce, ha da wani yaro mai kimanin shekaru 2 da rabi, wadanda duk ‘yan asalin Daura ne da ke jihar ta Katsina.
Ya ce sauran mutane 8 na nan na amsar kulawar likitoci kamar yadda aka tsara.
