Home Sabon Labari Katsina: PDP ta dakatar da Muttaqa Rabe Darma

Katsina: PDP ta dakatar da Muttaqa Rabe Darma

348
0

Jam’iyyar PDP a jihar Katsina reshen Wakilin kudu 1 ta kori jigon jam’iyyar a jihar kuma tsohon na hannun damar marigayi Umar Musa Yar’adua, Wato Engr Muttaƙa rabe Darma.

A wata takarda Mai dauke da sa hannun shugabannin jam’iyyar su 15 ta ce an dakatar da Muttaqa Rabe Darma ne bisa zargin yi wa jam’iyyar zagon-kasa. Jam’iyyar a matakin gunduma ta ce ta dakatar da dan siyasar na tsawan wata guda. Ta kuma aike wa da jami’an tsaro na ‘yan sanda da Civil Defence da kuma shugaban PDP na jihar Katsina takardar matakin da ta dauka na dakatar da tsohon shugaban hukumar PTDF din a Nijeriya.

Takardar dakatar da Muttaqa Rabe Darma daga PDP
Takardar dakatar da Muttaqa Rabe Darma daga PDP
Takardar dakatar da Muttaqa Rabe Darma daga PDP
Takardar dakatar da Muttaqa Rabe Darma daga PDP

A safiyar Juma’a ne dai wani sashe na jam’iyyar ya nemi ballewa bisa zargin tauye wa wasu ‘ya’yan jam’iyyar hakkinsu.

A taron manema labarai da ya samu halartat Muttaqa Rabe Darma da Lawal Rufa’i Safana ya gudanar, ya yi zargin cewa wasu tsiraru ne ke tafiyar da ragamar jam’iyyar ba tare da sun ba wasu dama ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply