Home Addini Katsina: Yadda aka mayar da Ukashatu mai shekaru 6 ya koma Michael...

Katsina: Yadda aka mayar da Ukashatu mai shekaru 6 ya koma Michael mai magana da Igbo

76
0

[cmsmasters_row data_shortcode_id=”roqd55hj” data_padding_bottom_mobile_v=”0″ data_padding_top_mobile_v=”0″ data_padding_bottom_mobile_h=”0″ data_padding_top_mobile_h=”0″ data_padding_bottom_tablet=”0″ data_padding_top_tablet=”0″ data_padding_bottom_laptop=”0″ data_padding_top_laptop=”0″ data_padding_bottom_large=”0″ data_padding_top_large=”0″ data_padding_bottom=”50″ data_padding_top=”0″ data_bg_parallax_ratio=”0.5″ data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center” data_color=”default” data_bot_style=”default” data_top_style=”default” data_padding_right=”3″ data_padding_left=”3″ data_width=”boxed”][cmsmasters_column data_width=”1/1″ data_shortcode_id=”hwz4ipczv” data_animation_delay=”0″ data_border_style=”default” data_bg_size=”cover” data_bg_attachment=”scroll” data_bg_repeat=”no-repeat” data_bg_position=”top center”][cmsmasters_text shortcode_id=”pbys8pkfpp” animation_delay=”0″]

Ba yau aka fara garkuwa da kananan yara Musulmai na Arewacin Nijeriya a mayar da su Kiristoci ba. A watan Maris na wannan shekara jaridar Daily Trust ta bayar da labarin wani yaro mai suna Ukashatu wanda yayi zargin wata mata ta yi kidindafin dinsa ta mayar da shi Igbo ta kuma sauya masa addini.

 

Malama Dahara ‘yar asalin Karamar Hukumar Baure ta jihar Katsina ita ce mahaifiyar Ukashatu, tana cikin mata makafi da ke bara a birnin Legas. Ta shaida wa DailyTrust cewa shekaru takwas ta kwashe ba tare da ganin Ukashatu ba.

Ta ce a wata rana a Unguwar Orile da ke Legas ta aiki yaron na ta ya zubar mata da shara da daddare to daga nan ta ji shiru bai dawo ba. Sai hankalinsu ya tashi suka bazama nemansa amma duk kokarin da suka yi na nemansa ba su gan shi  ba.

Ta ce yaron na ta ya bace lokacin da yake da shekaru 6 da haihuwa kuma tun daga lokacin take ta addu’ar Allah Ya bayyana shi. Kwatsam! A watan Maris din nan aka kira ta a waya zuwa ofishin ‘yan sanda aka sanar mata cewa an ga yaronta.

“kafin ‘yan sanda su ba ni Ukashatu sai da suka gwada, su tabbatar lallai nice mahaifiyarsa. Sai suka tsayar da ni daga nesa, shi kuma ya hango ni ya rugo da gudu ya rungume ni. Ina kuka shi ma yana kuka” Malama Dahara ta shaida wa DailyTrust

Da ake magana da Ukashatu ya shaida wa ‘yan jarida cewa wata mata ce mai suna Christiana Onuchukwu ta kira shi lokacin da mahaifiyarsa ta aike shi zubar da shara, inda Christiana ta yi masa kyautar burodi daga nan sai suka kama tafiya. Daga nan kawai sai ya gan shi a wani gida, matar ta ce masa ita ce mahifiyarsa kuma mijinta watau Mathew shi ne mahaifinsa. Haka aka ci gaba da zama har suka sanya shi a makarantar boko inda ya kai JSS1 kuma suka sauya masa suna ya koma Michael. Ta bangaren addini kuwa ya ce a duk ranar Lahadi ana shirya shi su tafi coci da shi da su Christiana. Shekaru 8 da ya kwashe a hannunsu sun sa babu wani harshe da yake iya magana da shi in ba Turancin Pidgin da Igbo ba.

Ukashatu dai ya ce duk da cewa yanzu bai iya yin hausa sosai amma dai yaji dadin dawowa cikin ‘yan uwansa.

 

[/cmsmasters_text][/cmsmasters_column][/cmsmasters_row]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply