Home Labarai Kebbi: Jami’an tsaro na DSS sun mika wa Gwamna Bagudu yaran da...

Kebbi: Jami’an tsaro na DSS sun mika wa Gwamna Bagudu yaran da aka sata zuwa Kudancin Nijeriya

82
0

Jami’an tsaro na DSS sun hannanta  wasu yara guda biyu wadanda ake zargin masu satar mutane suka sace a garin ZURU da ke jihar Kebbi.

An hannanta yaran ne ga Gwamnan jihar Kebbi Sanata  Abubakar Atiku Bagudu, inda ya mika su ga iyayensu.

Hotan wadanda ake zargi da satar yaran jihar Kebbi zuwa Kudancin Nijeriya

A cikin wadanda ake zargin  akwai mata guda biyu da suka fito daga jihar Anambra, daya kuma daga jihar Delta sai kuma namiji daya da ya fito daga garin na Zuru.

Gwamnan jihar ya jinjina wa hukumar tsaro ta DSS akan namijin kokarin da suke nunawa wajen samar da tsaro a jihar.  Gwamnan ya kuma  kara kira ga al’umma da su kula da yaransu  a kodayaushe da kuma saka ido ga sabbin fuskoki a unguwarsu.

[ditty_news_ticker id=”3203″]

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply