Home Labarai Kebbi: PDP ta ce “taka ‘ya’ya ga kaza ba kiyayya ba ce,...

Kebbi: PDP ta ce “taka ‘ya’ya ga kaza ba kiyayya ba ce, soyayya ce”.

74
0

Daga Abdullahi Garba Jani

Jam’iyyar PDP a jihar Kebbi da ke arewacin Nijeriya ta dage dakatarwar da ta yi wa wasu ‘ya’yanta su 14 bisa zarginsu da cin dunduniyar jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar na jiha Alhaji Haruna Sa’idu ya ce an dage dakatarwar da aka yi wa ‘ya’yan jam’iyyar na watanni 3 ne bayan saka baki da wasu dattawan jam’iyyar suka yi.

Idan za a iya tunawa dai, a ranar 5 ga watan Agusta, 2019, jam’iyyar ta dakatar da wasu ‘ya’yanta 14 bisa zargin yin zagon-kasa ga jam’iyyar.

Alhaji Haruna ya ce jam’iyyar na bukatar hadin kai domin ta kara ci gaban da aka san ta da shi.

Sannan ya ce jam’iyyar za ta shiga a dama da ita a zaben kananan hukumoni da za a gudanar jihar a watan Oktoba mai zuwa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply