Home Lafiya Kebbi ta hada hannu da Johnson&Johnson kan cutar HIV

Kebbi ta hada hannu da Johnson&Johnson kan cutar HIV

103
0

Gwamnatin jihar Kebbi arewacin Nijeriya ta soma bayar da wani horon kara wa juna sani ga ma’aikatan lafiya a jihar dangane da yadda za’a yaki cutar HIV/AIDS da kuma yadda za’a kula da lafiyar masu fama da tabin hankali.

Mahukumtan na Kebbi na gudanar da taron karkashin hadin gwiwar da suka yi da kamfanin hada magunguna na Amirka da ake kira Johnson and Johnson. Sanarwar da hukumomi suka fitar sun ce za a kwashe kwanaki hudu ana wannan taro.

Taron ma’aikatan kiwon lafiya na Kebbi

Gwamnatin dai ta ce musayar bayanai tsakanin jami‘an  wannan kamfanin har-hada magun-guna da ma’aikatan lafiya zai taimaka ga samar da makamar aiki ga dalibbai masu koyon aiki likita da zai taimaki jihar har illa masha Allahu, kamar yadda Mataimaki na musamman kan harkar yada labarai ga gwamnan jihar Kebbi Malam Yahaya Sarki ya tabbatar a cikin sanarwar da ya fitar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply