Home Lafiya Kebbi: zuwa awo na inganta lafiyar mata masu juna biyu-inji Gwamna Bagudu

Kebbi: zuwa awo na inganta lafiyar mata masu juna biyu-inji Gwamna Bagudu

64
0

 

Rahma Ibrahim Turare/Jani

Gwamnan jihar Kebbi Abubakar Bagudu ya yi kira ga shugabannin al’umma da su rika karfafa wa mata masu juna biyu guiwa da su rika ziyartar cibiyar kula da lafiya a yankunansu domin yin awo kafin haihuwa.

Atiku Bagudu ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke kaddamar da cibiyar kula da lafiya a matakin farko da aka daga darajarta a Bachaka da ke karamar hukumar Arewa,wadda aka daga darajarta.

Ya zuwa yanzu, gwamnatin jihar ta daga darajar cibiyoyin kiwon lafiya guda 225 domin samar da ingantacciyar lafiya ga al’umma.

Gwamnan ya yi kira ga al’ummomi, musamman mata masu juna biyu da kananan yara da su rika ziyartar asibitoci domin samun ingantaciyar lafiya.

Kamar yadda gwamnan yace, sama da cibiyoyin kiwon lafiya guda 20 acikin 225 an gyara su ne tare da hadin gwiwar asusun kula da kananan yara na majalisar dunkin duniya UNICEF.

Ya bayyana cewa gwamnati tare da UNICEF sun hada gwiwa da kungiyar direbobi(NURTW)domin daukar mata masu juna biyu zuwa cibiyoyin kiwon lafiya kyauta domin inganta lafiyarsu.

A jawabinta uwargidan gwamnan Dr.Zainab Bagudu ta ba mata shawara da su dauki dabi’ar haihuwa a asibiti, ta ci gaba tana cewa akwai asibitocin a wadace a duk daukacin kananan hukumomi 21 da ke a fadin jihar .

Ta kuma shawarci matan da su rungumi sana’oi domin samun kudaden shiga.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply