Masu bincike a kasar Kenya za su ba da shawarar hukunta jami’an gwamnati su 15 da ma wasu ‘yan kasuwa saboda zarginsu da karkatar da kudaden da yawansu ya kai kimanin Dalar Amurka milyan dubu biyu da gwamnatin kasar ta ware domin sayo kayayyakin yaki da cutar corona.
Bincike ya gano hujjoji da aka gabatar na zargin wasu manyan ‘yan siyasar kasar da ‘yan kasuwar da laifin karkatar da wadannan kudade da suka yi batan-dabo.
Gwamnati ta ba da umurnin a gudanar da bincike biyo bayan samun korafe-korafe daga jama’a kan zargin wadannan mutane da wawure wadannan makuden kudade.
