Home Kasashen Ketare Kenya: an kori wata ‘yar majalisa saboda ta zo da jariri

Kenya: an kori wata ‘yar majalisa saboda ta zo da jariri

74
0

Daga Abdullahi Garba Jani/NIB

An kori Zulekha Hassan ‘yar majalisar dokoki a kasar Kenya daga zauren majalisar sabo da ta halarci zaman majalisar da jaririnta sabon haihuwa.

Jaridar Punch ta rawaito cewa Zulekha Hassan na wakiltar yankin Kwale ne kudu maso yammacin birnin Mombasa na kasar Kenya.

Zulekha Hassan yar majalisar Kenya

Mrs Hassan dai ta halarci zaman majalisar ne da jaririn ta bisa dalilin ta na cewa bata samu isasshen lokacin da za ta kai shi wajen masu raino ba saboda kiran gaggawa da aka yi masu.

Majalisar kuwa ta tsaya kai da fata kan cewa, dokar majalisar ba ta aminta da bako ko da kuwa jariri ne ya shiga har cikin zauren majalisar ba.

Kungiyoyin kare hakkin mata na ci gaba da fafutika tare da yekuwar neman a sakar wa mata mara don gudanar da harkokin su kamar yadda kowa ke yi.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply