“Kidinafas mutanen banza ne” inji Gwamna Nasiru Elrufai na jihar Kaduna.
Gwamnan a cikin tattaunawar da yayi da ‘yan jarida a yammacin Juma’a ya ce akwai bukatar mutane su kara ba su goyon baya a kokarin da suke yi na samar da tsaro a jihar Kaduna.
DCL Hausa ta kalli bidiyo na Facebook Live da Gwamnan ya wallafa a shafinsa: https://m.facebook.com/story.php?story_fbid=1505314816302051&id=393816480127
Elrufai ya ce ya kirkiro ma’aikata ta musamman don magance matsalar tsaro a karkashin Samuel Aruwan. Ya ce ya gamsu da ci gaban da ake samu a wurin ci gaban tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.
Akwai bukatar ya sake dabara? Wace gudunmawa ya kamata ‘yan jihar Kaduna su ba shi don murkushe kidinafin a Rigasa da Chikun da Birnin Gwari?
