Home Sabon Labari Kidinafas sun saci Hakimi da dansa a jihar Zamfara

Kidinafas sun saci Hakimi da dansa a jihar Zamfara

108
0

Yan bindiga sun yi garkuwa da  Hakimin Gayari a cikin Karamar Hukumar Gumi da ke jihar Zamfara.  Wani mazanin Gayari Malam Abubakar Sani ya shaida wa jaridar The Punch cewa ‘yan bindigar sun shiga garinsu a jiya alhamis da daddare kuma kai tsaye suka nufi gidan hakimi inda suka yi garkuwa da shi da dansa.

Jaridar ta ce ‘yan bindigar sun rike bindiga samfurin AK47 suna harbawa a saman iska don tsorata jama’an garin wadanda suka so ceto basaraken.

Magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara SP Shehu ya sahida wa ‘yan jarida cewa har yanzu ba su kai ga samun wannan labari ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply