Home Sabon Labari Kidinafin: An sace wani malamin jami’ar FUDMA a Arewacin Nijeriya.

Kidinafin: An sace wani malamin jami’ar FUDMA a Arewacin Nijeriya.

70
0

Daga Abdullahi Garba Jani

Rahotannin daga Kaduna Arewacin Nijeriya sun nuna cewa an sace Malam Abubakar Idris, malami a jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsin-ma, jihar Katsina -FUDMA.

A ranar Asabar din nan, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kaduna DSP Yakubu Sabo ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce rundunar ‘yansandan ta samu labarin ne ta hannun babban baturen ‘yansanda -DPO- na yankin Barnawa, Kaduna cewa wasu da ba a san ko su wanene ba, sun kutsa kai gidan malamin inda suka yi awon-gaba da shi.

DSP Sabo ya ce da jin wannan batu sai ‘yansandan da ke sintiri na Patrol suka hanzarta kai dauki, wanda kafin su isa, mutanen sun tsere da shi.

Ya ce daga bisani sai bincike ya nuna cewa an sace malamin ne a kan hanyarsa ta komawa gida da misalin karfe dayan dare.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply