Home Sabon Labari Kidinafin: Masari ya ce mutane na son daukar makamai su nufi...

Kidinafin: Masari ya ce mutane na son daukar makamai su nufi ‘yan bindiga

301
0

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ce a cikin makonni biyun da suka gabata kusan kowace rana sai an kai hari a wani kauye a cikin yankunan karkarar jiharsa da ke fama da rikicin ‘yan bindiga.

Ya shaida wa Manjo Janar Leo Irabor babban jami’in rundunar sojin kasa ta Nijeriya a ranar Alhamis din nan cewa a baya-bayan nan akalla mutane 50 ‘yan bindiga suka hallaka a wadannan wurare.

Aminu Masari Gwamnan jihar Katsina

Ya ce a don haka mutanen yankunan kamar Faskari sun lashi takobi gara su dauki makami su bi ‘yan bindiga a cikin daji koda kuwa za su rasa rayukansu. Gwamna Masari ya ce da kyar da jibin goshi ya samu ya lallashi mutanen suka canza shawarar tunkarar ‘yan bindiga, domin dai ‘yan bindigar na da makaman da a wasu lokuttan yafi na jami’an tsaro hadari.

Gwamna Masari ya ce yanzu da shi da mutanen yankunan sun zura ido su ga abin da jami’an tsaro za su iya yi a kan wannan matsala.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply