Home Addini Kirsimeti: ‘Yan Shi’a sun kai kyautukan bukukuwan kirsimeti a coci-coci

Kirsimeti: ‘Yan Shi’a sun kai kyautukan bukukuwan kirsimeti a coci-coci

95
0

Abdullahi Garba Jani

Wasu mabiya mazhabar shi’a sun halarci coci a Samaru ta Zariya ta jihar Kaduna inda suka bi sahun kiristoci aka yi adu’o’i don bikin ranar Kirsimeti da su a ranar Larabar nan.
Da ya ke ganawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya, shugaban tawagar Prof. Isah Hassan-Mshelgaru ya ce babban makasudin ziyarar shi ne su kara dankon zumunci da kaunar juna a tsakanin ‘yan Nijeriya.
An dai gudanar da adu’o’in cocin ne a majami’ar Anglican da ke Samaru, Zariya a jihar Kaduna, inda Prof Hassan-Mshelgaru ya yi roko ga ‘yan Nijeriya da a kodayaushe su cire bambancin addini ko na al’ada a tsakani, ya ce addini na nufin hada kai da kaunar juna.
Babban limamim cocin, Rev. Isuwa Sa’idu, ya nuna jindadinsa bisa ziyarar, har ma ya roki mabiya mazhabar shi’ar da su dore da irin wadannann ziyarori. Ya ce wannan ziyarar ta nuna cewa ‘yan Nijeriya masu so da kaunar zaman lafiya.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply