Home Labarai Ko da gaske ne Malam Ali na fim din kwana casa’in ya...

Ko da gaske ne Malam Ali na fim din kwana casa’in ya auri yar shekaru 60?

111
0

Ahmadu Rabe Yanduna

Safiyar Asabar wasu hotuna suka fara yawo a shafukan sada zumunta na jarumin shirin ‘Kwana Casa’in’ Abdul’shahoor wanda aka fi sani da Malam Ali tare da wata ‘yar takarar Sanata daga jihar Kaduna mai suna Bilkisu Shibah Sulaiman, cikin yanayin da ke nuna suna shirin aure ko kuma sun yi auren a yadda hotunan suka nuna.

Bayyanar wadannan hotunan a kafar sadarwa ya dauki hankalin jama’a da dama matuƙa, inda Jama’a suka rinƙa tsegumi bayan ganin hotunan duba da tazarar shekarun da ke tsakanin masoyan guda biyu, a ya yin da wasu ma ke karyata wannan lamari, wasu kuma sun yarda cewa zai iya faruwa.

Bayan bayyanar wadannan hotunan na Malam Ali da tsohuwar yar takarar sanata a Jihar Kaduna sai Malam Alin ya saki wani ɗan takaitaccen faifan bidiyo a shafin sa na Facebook inda ya gaskata lamarin cewa aure suka yi a daina yaɗa batun a matsayin jita-jita.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply