Home Coronavirus “Kodai ‘yan Nijeya su mutumta dokokin corona, ko kuma mu rufe kasar...

“Kodai ‘yan Nijeya su mutumta dokokin corona, ko kuma mu rufe kasar nan”- Gwamnatin Buhari

55
0

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari  ya ce ya damu matuka da yadda yake samun rahotannin cewa ‘yan Nijeriya ba sa mutumta dokokin corona, da suka hada da sanya takunkumi da barin tazara a al’amurran yau da kullum.

A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yada Labarai na Fadar Shugaban Kasa, Garba Shehu ya fitar a yammacin wannan Lahadi ya ce Shugaba Buhari ya sanya hannu a kan umurnin shugaban kasa domin sanya ‘yan Nijeriya bin dokokin corona ba wai domin kuntata wa jama’a ba, kamar yadda jaridar DCL Hausa ta ruwaito.

Garba Shehu ya ce idan har ‘yan Nijeriya suka ci gaba da kin mutumta dokokin kare kai daga COVID-19 to babu abin da zai hana gwamnati sake rufe kasar nan.

Sai dai wannan labain na zuwa ne ‘yan sa’o’i kadan bayan da babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta soki Shugaba Buhari kan ganin hotansa babu takunkumi a cikin jama’a a wurin rajistar ‘yan jam’iyyar APC a Daura a ranar Asabar.

 

Labari Mai Alaka:

PDP ta yi tir da Buhari saboda karya dokar Covid-19

Ba za a kara saka dokar kulle ta “lockdown” ba – FG

Za a sake kafa dokar kulle a Nijeriya

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply