Ma’aikatar harkokin addinin musulunci ta kasar Saudiyya tare da ma’aikatan ta, na shitin fara tsabtace sama da masallatai 90,000 da za a bude ranar Lahadi a fadin kasar in banda birnin Makkah.
Wannan na zuwa ne bayan an rufe manya da kananan masallatan kasar sama da watanni biyu, biyo bayan bullar cutar Covid-19.
Bude masallatan dai zai kasance ne karkashin tsarin ministan harkokin addinin musulunci na kasar Dr. Abdullatif Al-Asheikh da kuma shawarwarin da babbar majalisar malaman kasar ta bayar.
Tuni dai ma’aikatar ta fara gangamin wayar da kai a kafafen yada labarai kan yadda masu zuwa ibada za su dau matakan kariya don dakile yaduwar cutar.
