Home Labarai Kotu a Kaduna ta dage shariar Malam Zakzaky

Kotu a Kaduna ta dage shariar Malam Zakzaky

151
1

Shariar Zakzaky:KOTUN KADUNA TA DAGE ZAMAN DUBA YIWUWAR  FITARSA WAJE JINYA.

A yau alhamis babbar kotun jihar Kaduna ta dage zaman tattauna bukatar jagoran yan shia Ibrahim Zakzaky ta barinsa zuwa kasar Indiya don kula da kafiyarsa.

Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa bacin shi kansa jagoran na yan shiar ya so a bar matarshi, Malama Zeenatu itama ta tafi Indiya don ganin likita.

Tun a jiya laraba mai lauyan gwamnatin jihar Kaduna Mr. Dari Bayero ya fadawa yan jarida cewa kotu za ta saurari wannan bukata ta Zakzaky.

A baya bayan nan yan shia na zargin an sanyawa malamin nasu guba don cimma wata manufa, zargin da har yanzu likitoci a nan Najeriya ba su kai ga tabbatar wa ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

1 COMMENT

Leave a Reply