Home Labarai Kotu: An gurfanar da matar da ta jefa danta rijiya

Kotu: An gurfanar da matar da ta jefa danta rijiya

70
0

Abdullahi Garba Jani

Wata mata mai shekaru 33 mai suna Ruqayyat AbdulRaheem ta gurfana a gaban kotun Majastare da ke zamanta a birnin Osogbo bisa tuhumar jefa danta cikin rijiya.

Bincike ya gano cewa Ruqayyat ta jefa danta mai suna AbdulGaniyu cikin rijiya da hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Kamar yadda bayanai suka nuna, Ruqayyat ta jefa yaron a rijiya ne a ranar 17 ga watan Nuwamba, 2019 da misalin karfe 5:30 na safiya a kan layin Tokolaya, a birnin Osogbo.

Laifin dai ya ci karo da kundin doka na 319 karamin sashe na 1 na penal kod.

Duba da girman laifin dai ya sa ba a karbi tubar da wadda ta aikata laifin take yi ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply