Home Addini Kotu ta ba da umurnin a ci gaba da tsare Zakzaky

Kotu ta ba da umurnin a ci gaba da tsare Zakzaky

216
0

Wata kotu a Kaduna ta ba da umurnin a ci gaba da tsare jagoran mazhabar Shi’a Ibrahim El Zakzaky.

A yau Juma’a ne aka kotun ta sake sauraron karar, sai dai alkalin kotun ya bayyana ranar 29/9/2020 a matsayin ranar da zai yanke hukunci kan shari’ar, wato nan da kwanaki 53 masu zuwa.

Zakzaky dai na cigaba da rayuwa a gidan jarum tun bayan arangamar da aka yi tsakanin Sojoji da mabiyanshi a shekarar 2015.

Bisa ga hukuncin da alkalin ya zartar a yau, jagoran ‘yan Shi’an zai ci gaba da zama a gidan kaso har ya zuwa karshen watan tara na wannan shekara ta 2020 da muke ciki.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply