Home Labarai Kotu ta ba magidanci zabin zaman kaso na watanni 18 ko biyan...

Kotu ta ba magidanci zabin zaman kaso na watanni 18 ko biyan N60,000 a Legas

73
0

Wata babbar kotun tarayya da ke a jihar Legas ta yanke wa wani mutum mai suna Prince Anyanwu dan shekaru 49, hukuncin daurin watanni 18 a gidan gyaran hali bisa zarginsa da safarar miyagun kwayoyi.

Hukumar hana sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) ce ta gurfanar da Anyawu a gaban kotun a ranar 16 ga watan Nuwamba nan, inda ake tuhumarsa da fataucin tabar wiwi.

Sai dai alkalin kotun ya bayar da zabi ga Anyanwu ko dai a kai shi ya shafe watanni 18 a gidan maza ko kuma biyan tarar N60,000.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply