Home Labarai Kotu ta bada belin Ndume

Kotu ta bada belin Ndume

120
0

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ba da belin Sanata mai wakiltar Borno ta kudu, Ali Ndume, wanda aka tsare a kurkuku tun ranar Litinin.

Alkalin Kotun mai Shari’a Okon Abang a hukuncin da ya yanke a Juma’ar nan, ya ce ya yanke shawarar ba da belin Sanata Ndume ne saboda tarihinsa na mutum mai halayya tagari amma ba don uzurorin da ya gabatar ba.

Alkali ya ba shi beli ne kafi kotun daukaka kara ta saurari karar da Ndume ya shigar ranar Litinin domin kalubalantar hukuncin jefa shi kotu kan gaza kawo Maina kotu.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply