Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bada umarninsoke belin tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho Abdulrasheed Maina.
Alƙali Okon Abang ta bada umarnin a zaman kotun na ranar Laraba tare da bada umarninna kama Maina a duk inda aka same shi.
Da yake gabatar da buƙatar soke belin lauyan EFCC Muhammad Abubakar, ya shaida wa kotun cewa Maina, ya karya ƙa’idojin belin da aka ba shi kan Naira milyan 500 tare da gabatar da Sanatan da zai tsaya masa.
