Home Labarai Kotu ta dakatar da babban taron PDP

Kotu ta dakatar da babban taron PDP

258
0

Wata babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ta ba da umurni na wucin-gadi da a dakatar da jam’iyyar PDP daga yin gangamin taron zaben shugabannin jam’iyyar dama wakillanta na kananan hukumomi a jihar Kano.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa akalin kotun, mai shari’a Lewis Allagoa ne ya gabatar hukuncin a ranar Litinin din nan.

Ya kuma dakatar da babban sufeton ‘yan sanda dama hukumar zabe ta INEC da kada su amince a gudanar wannan babban taron, har sai an yanke hukunci a kan karar da daya daga cikin masu neman mukamin shugabancin jam’iyyar a jiha Ali Baffa dama wasu mutane biyu suka shigar saboda soke sunayensu daga cikin wadanda za su fafata a zaben.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply