Home Labarai Kotu ta daure wasu mutane saboda satar taliya indomie a Nijeriya

Kotu ta daure wasu mutane saboda satar taliya indomie a Nijeriya

82
0

Babbar kotun jihar Ekiti da ke zamanta a birnin Ado Ekiti ta yanke hukuncin daurin shekaru 7 ga wasu mutane 4 da suka saci taliyar Indomie da taba sigari ba tare da zabin biyan tara ba.

Mutanen da aka kama da laifi su ne Owoeye Ojo, Agbetuyi Taiwo, Adeniyi Busayo da Lasisi Friday.

An dai kama mutanen da laifin barke wani shago na wata mata mai suna Iyabo Ige a ranar 26 ga watan Agusta, 2017a birnin Ado Ekiti.

Jaridar Punch ta wallafa cewa mutanen sun yi awon-gaba da kwalayen taliyar Indomie da na taba sigari da madara da sauran abubuwa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply