Home Labarai Kotu ta fara sauraron ƙara kan naɗin sarkin Zazzau

Kotu ta fara sauraron ƙara kan naɗin sarkin Zazzau

257
0

Babbar kotun jihar Kaduna ƙarƙashin jagorancin Alƙali Kabir Dabo, wadda ke Dogarawa Sabon Gari, ta fara sauraron ƙarar da aka shigar kan naɗin Ahmad Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau da gwamna Nasir El-Rufa’i ya yi.

Daily Trust ta ruwaito cewa ɗaya daga cikin masu neman sarautar ne, Bashar Aminu, ya shigar da ƙarar.

Aminu dai shi ne wanda ke kan gaba cikin mutum huɗu na farko da masu zaɓen sarkin suka tura wa gwamnan, kafin daga bisani a sake tura wani jerin sunayen da aka haɗa da sunan Bamalli a ciki.

Aminu, ya nuna cewa sake tura wasu sabbin sunayen bayan wanda aka tura da farko, ba adalci bane.

Yanzu dai an ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 27 ga watan Oktoba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply