Abdullahi Garba Jani
Kotun daukaka kara a Nijeriya ta soke zaben dan majalisar wakilai na kasar mai wakiltar kananan hukumonin Kiru/Bebeji a jihar Kano, inda ta ba da umurnin da a sake sabon zabe.
Kotun ta yanke hukuncin cewa duk sakamakon zaben da aka gudanar a kananan hukumomin biyu bai inganta ba.
Idan za a iya tunawa dai a ranar 12 ga watan Satumba na wannan shekarar ne kotun sauraren kararrakin zabe ta tabbatar da nasarar da Abdulmumin Jibrin ya yi a zaben 27 ga watan Fabrairu.
Mr Yako da jam’iyyar PDP dai, sun maka Abdulmumin Jibrin a kotu, inda suke kalubalantar nasarar da ya yi bisa zargin an yi magudi.
Mr Yako ya yi zargin cewa hukumar INEC ta yi kuskuren ayyana Abdulmumin Jibrin a matsayin wanda ya yi nasarar lashe zaben da kuri’u 41,700 a ya yin da aka tabbatar ya samu kuri’u 40,385.
