Home Labarai Kotu ta tabbatar da zaben Masari a matsayin gwamnan jihar Katsina

Kotu ta tabbatar da zaben Masari a matsayin gwamnan jihar Katsina

76
0

Abdullahi Garba Jani

Kotun daukaka kara a Kaduna, ta kori karar da dan takarar gwamnan jihar Katsina a karkashin jam’iyyar PDP Sanata Yakubu Lado Danmarke ya shigar kan gwamna Aminu Masari, jam’iyyar APC ta jiha da hukumar zabe ta INEC.

Rahotanni sun ce dukkanin alkalan da suka jagoranci karar sun aminta da korar ta.

Kotun ta fara sauraren karar ne a ranar Talata. Bayan sauraron bahasi daga bangarorin biyu, kotun ta dage zamanta sai Alhamis din nan.

Yakubu Lado Danmarke dai na kalubalantar nasarar da gwamna Aminu Masari ya samu a zaben 2019.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply