Home Labarai Kotu ta umurci EFCC ta kamo Diezani

Kotu ta umurci EFCC ta kamo Diezani

71
0

Babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bukaci hukumar EFCC da ta gurfanar mata da tsohuwar ministar man fetur ta Nijeriya a gabanta don tuhumarta kan zargin wawure kudaden gwamnati a ranar 3 ga watan Maris na 2021.

Alkalin kotun mai shari’a Ijeoma Ojukwu dai, tun a 24 ga Juli, 2020 ya ba da umurnin da a gabatar wa kotu da Diezani Alison Madueke domin fuskantar tuhume-tuhume.

Amma dai Diezani Madueke wadda ake kyautata zaton ta arce daga kasar ta koma kasar Ingila, ta yi kememe ta ki amsa goron gayyatar kotun.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply