Kotun Majastare da ke zamanta a Yaba jihar Legas ta wanke yarinya mai kimanin shekaru 15 da ta kashe wani dan shekaru 51 da ya yi yunkurin yi mata fyade.
Alkalin kotun Philip Adebowale Ojo ya kori karar da ‘yansanda suka shigar kan yarinyar ‘yar aji ukun babbar sakandare.
Lauyan da ya ke kare yarinyar ya nuna gamsuwarsa bisa wannan mataki na kotun.
