Home Labarai Kotu ta yanke mata hukuncin kisa saboda ta kashe mijin ta a...

Kotu ta yanke mata hukuncin kisa saboda ta kashe mijin ta a Kano

72
0

Babbar kotun jihar Kano karkashi jagoracin Alkali A. T. Badamasi ta yankewa wata matar aure ‘yar kimanin shekaru 35 hukuncin kisa ta hanyar rataya a jiya Juma’a.

An yankewa Rashida Sa’idu wadda ke zaune a unguyar Dorayi hukuncin ne, saboda kama ta da laifin kashe mijin ta, ta hanyar turo shi daga saman bene.

Lauya mai gabatar da kara Maryam Jibirin ta ce wadda aka yankewa hukuncin ta aikata laifin ne a ranar 25 ga watan Fubrairun 2019.

Ta ce a ranar ne da misalin karfe 8pm na dare, Rashida ta zargi mijin ta Adamu Ali dan shekara 53 da cin amanar ta, a wata waya da ta ji yana yi, kuma nan take suka fara fada a cikin gidan na su, na Dorayi, wanda ya yi sanadiyyar ta angazo shi daga saman bene.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply