Home Labarai Kotu ta yankewa Olisa Metu hukuncin daurin shekara 7, ta ci kamfanin...

Kotu ta yankewa Olisa Metu hukuncin daurin shekara 7, ta ci kamfanin sa tarar N25m

67
0

Wata kotun tarayya da ke Abuja ta yankewa tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP Olisa Metuh hukuncin shekaru 7 a gidan yari, saboda kama shi da laifi a zarge-zarge 7 da ake yi masa.

 

Da yake yanke hukunci a ranar Talatar nan, Alkali Okon Abang, ya bada umarnin Metuh ya biya gwamnatin tarayya Naira miliyan 366.

Sannan kuma kamfanin sa Destra Investment Ltd. zai biya tarar Naira miliyan 25.

Alkalin ya ce ya fuskanci muzgunawa daga bangaren lauyoyi da kafafen yada labarai, tsawon shekaru hudu da aka yi ana wannan shari’a.

Ya ce Metuh ya nuna tsaurin kai wajen kin amsa laifin da EFCC ke tuhumar sa, har zuwa zargin bada toshiyar Naira miliyan 50 ga matar sa.

Tun da farko dai Alkali Abang ya kama Metuh da laifi kan zarge-zarge 7 da hukumar EFCC ke tuhumar sa, wadanda ke da alaka da karbar Naira miliyan 400 daga tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Kanal Sambo Dasuki, lamarin da Metuh ya sha musantawa.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply