Home Lafiya Kotu za ta raba mu da babban sufeton ‘yansanda – Tsohon Sarkin...

Kotu za ta raba mu da babban sufeton ‘yansanda – Tsohon Sarkin Maru

129
0

Tsohon Sarkin Maru a jihar Zamfara Alhaji Abubakar Ibrahim ya maka babban sufeton ‘yansandan Nijeriya Mohammed Adamu da wasu mutane 5 a gaban kotu bisa zargin tsare shi ba bisa ka’ida ba da kuma bata masa suna.

A shekarar bara ne dai gwamna Bello Matawalle na jihar ya sauke sarkin bisa zargin yana taimakon ‘yan ta’adda a jihar.

Sauran mutane 5 da ya ke kara sun hada da shugaban hukumar tsaron ciki DSS, kwamishinan ‘yansanda na jihar, da mataimakin shugaban hukumar DSS da sakataren gwamnatin jihar Zamfara Alhaji Bala Maru.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply