Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Kotun Birtaniya ta yi watsi da ƙarar Nijeriya kan Shell da ta...

Kotun Birtaniya ta yi watsi da ƙarar Nijeriya kan Shell da ta kai $1bn

131
0

Wata kotu a kasar Birtaniya ta ce ba za ta ci gaba da sauraron karar Nijeriya da kamfanin mai na Shell da Eni da ta kai Dala Biliyan daya ba, saboda ba ta da hurumin sauraron karar.

Alkalin kotun Christopher Butcher ya yanke wannan hukunci a wani kwarkwaryan zama da aka gudanar ranar Juma’a domin kawo karshen wannan doguwar shari’a kan dakalar man Malabu da aka faro tun shekarar 2011.
Haka kuma, an hana Nijeriya daukaka kara kan wannan hukuncin.
An hana wannan bukata ne, bayan da kamfani Enid a Shell suka nuna rashin amincewa da bukatar Nijeriyar na daukaka karar, saidai duk da haka Nijeriya za ta iya sake mika bukatar neman amicewa ta daukaka karar.

Kamfanonin dai sun bukaci kotun ta bayyana ba ta da hurumin sauraron karar saboda shariyar da ake gudanarwa ta kamfanonin a kasar Italiya har yanzu.
Saidai wannan hukuncin bai shafiy zarge-zargen da ake yiwa kamfanonin ba a kasar Italiya, wanda har yanzu ake ci gaba da shari’ar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply