Home Kasashen Ketare Kotun Nijar ta sanar cewa Bazoum ke kan gaba a sakamakon karshe...

Kotun Nijar ta sanar cewa Bazoum ke kan gaba a sakamakon karshe na zaben shugaban kasa

42
0

Kotun kundin tsarin mulkin jamhuriyar Nijar ta bayyana sakamakon karshe na zaben shugaban kasa da ya wakana na ranar 27 ga watan Disambar da ya gabata na shekarar bara, 2020.

A yayin wani zamanta ne a daren Asabar a babban birnin Yamai, kotun ta sanar da kammala sakamakon karshen da aka jima ana jira.

Yadda zaman kotun na karshe ya gudana

Sakamakon kuma ya nuna dan takarar jam’iyya mai mulki ta PNDS malan Bazoum Mohamed ne ke kan gaba da kaso 39,30 cikin dari sai dan takarar jam’iyyar RDR Tchanji Mahaman Ousman da yake rufa mishi baya da 16,98 cikin dari lamarin kuma da ya nuna za a tafi zagaye na biyu kamar yadda sakamakon wucin-gadi na hukumar zaben CENI ya nuna.

Tun a ranar 2 ga wannan wata ne dai hukumar zaben ta bayyana sakamakon wucin-gadin na zaben zagaye na farko ta kuma mika shi ga kotun kundin tsarin mulkin a ranar 4 ga watan.

Dama, a dokance kotun kwanaki 28 ke gare ta domin tantance sakamakon da hukumar ta gabatar mata.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply