Ƙungiyar malaman jami’o’in Nijeriya ASUU ta buƙaci ɗaliban jami’o’in musamman na aji 3 da 4 kan su hanzarta fara karatu.
Ƙungiyar wadda ta bayyana haka a wani saƙon twitter da ta wallafa a ranar Asabar, ta ce akwai yiwuwar da zarar an koma aiki ɗaliban za su fara jarabawa ne nan take.
A don haka ASUU ta shawarce su, da su ta samma karatu gadan-gadan ba kama hannun yaro.
