Home Labarai Ku ba matasa dama a shugabancin Nijeriya – Obasanjo

Ku ba matasa dama a shugabancin Nijeriya – Obasanjo

267
0

Tsohon shugaban kasar Nijeriya Chief Olusegun Obasanjo, ya yi kira ga matasa da su yi duk abin da ya kamata don ganin sun amshi mulki daga hannun dattawa.

Obasanjo ya kuma bukaci matasan da su shiga harkar siyasa gadan-gadan domin tsara yadda za su ya kamata su karbi ragamar shugabanci a dukkanin matakai.

A cikin jawabin maraba da ya gabatar a taron tunawa da ranar matasa ta duniya, Obasanjo ya ce muddin matasa ba su tashi tsaye ba, to kuwa za su ci gaba da cin tuwo da miyar bara.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply