Home Kasuwanci/Tattalin Arziƙi Ku daina ɗora mana laifin matsalarku – Sirika ga kamfanonin jirage

Ku daina ɗora mana laifin matsalarku – Sirika ga kamfanonin jirage

107
0

Minista sufurin jiragen sama Sanata Hadi sirika, ya gargaɗi kamfanonin jiragen sama dake aiki Nijeriya kan ɗora alhakin rashin samun riba da rashin kyakkyawan yanayin aiki da suke fuskanta a Nijeriya ga hukumomin dake kula da harkokin sifirin.

Sirika ya yi gargaɗin ne ranar Alhamis a ƙarshen taron sauraron ra’ayoyin jama’a na kwana uku da Majalisar dattawa ta shirya kan wasu ƙudirori 6 na gyaran fasalin sufurin saman.

Ministan yana maida martani ne kan iƙirarin da kamfanonin suka yi na cewa suna fuskantar wahalar kasuwancinsu a Nijeriya ne saboda rashin kyawawan dokokin gwamnati a ɓangaren.

Shugaban kamfanin jiragen sama na Overland Airways Kyaftin Edward Boyo, ya ɗora alhakin wahalar da ɓangaren ke ciki ga hukumomin da ke kula da sufurin saman.

Yana mai cewa saka haraji ba gaira ba dalili da hukumar kula da jiragen sama haɗin guiwa da ma’aikatar sufurin saman ya janyo tsadar tikitin jirgi a ƙasar, inda ya ce hakan kuma ya fi shafar kamfanonin cikin gida ne.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply