Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga shugabannin kasashen yammacin Afirka da su guji son tsawaita zama akan madafun iko.
Shugaba Buhari ya yi wannan kira ne yayin da yake gabatar jawabinsa a taron da shugabannin kungiyar ECOWAS da aka gudanar a birnin Yamai na jamhuriyar Nijar.
Ya kuma bukaci takwarorinsa da su rika mutunta kundin tsarin mulki na kasashen su, domin tabbatar da dorewar dimokaradiyya a nahiyar ta Afirka.
