Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga ’yan NIjeriya da su duba tare da tantance alkawuran da ’yan siyasa ke yi kafin su yanke shawarar wanda za su kada wa kuri’a a babban zaben shekarar 2027.
Ya kuma gargadi ’yan siyasa da kada su mayar da matsalar rashin tsaro da sauran kalubalen da kasar ke fuskanta kayan yakin neman zabe, inda ya bukace su da su mayar da hankali kan batutuwan da za su taimaka wajen samar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaban kasa.
Sarkin Musulmin ya bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da ya karbi bakuncin kwamitin yakin neman zaben jam’iyyar APC na shekarar 2027, karkashin jagorancin Darakta-Janar dinsa, Sanata Abdul-Aziz Yari Abubakar, a fadarsa da ke Sokoto.
Ya ce ya kamata masu kada kuri’a su saurari alkawuran ’yan siyasa da kyau a lokacin yakin neman zabe, sannan su zabi wanda suke ganin manufofinsa za su fi amfani ga muradunsu da kuma ci gaban kasa.
Sarkin Musulmi ya bukaci jam’iyyun siyasa da ’yan takararsu da su gudanar da yakin neman zabe cikin lumana, su mayar da hankali kan batutuwa masu muhimmanci, su mutunta zabin masu kada kuri’a, sannan su gudanar da siyasa ta hanyar da za ta karfafa hadin kan kasa da ci gabanta.
Ya ce babu wata gwamnati a duniya da za ta iya kawar da matsalar rashin tsaro da talauci gaba daya, amma gwamnati na iya yin kokari wajen rage illolin da wadannan matsaloli ke haifarwa ga al’umma.
Sarkin Musulmi ya yi wa mambobin kwamitin yakin neman zaben APC fatan samun nasara, tare da yin addu’ar samun ci gaba da zaman lafiya, kwanciyar hankali da shugabanci nagari a NIjeriya.
Tun da farko, Sanata Yari ya ce tawagar ta je fadar Sarkin Musulmi ne domin neman shawararsa, jagorancinsa na uba da kuma addu’o’insa gabanin babban zaben shekarar 2027.
Yari ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tun kafin ya zama shugaban kasa, ya nuna jajircewarsa wajen bunkasa Arewa da NIjeriya baki daya, ta hanyar tallafa wa wasu shugabanni da kuma shirye-shiryen ci gaba.
Ya ce gwamnatin tarayya karkashin jagorancin APC tana da nasarori da dama da za ta gabatar wa ’yan Najeriya, musamman a karkashin gwamnatin Shugaba Tinubu.
A cewarsa, gwamnatin ta ci gaba da jajircewa wajen inganta zaman lafiya, hadin kai da dunkulewar al’ummar NIjeriya.
Yari ya tabbatar wa Sarkin Musulmi cewa jam’iyyar za ta gudanar da yakin neman zabe cikin lumana, sannan ya roki ci gaba da goyon bayansa da addu’o’insa.
Shi ma Gwamnan Jihar Sokoto, Dakta Ahmed Aliyu, ya ce tsarin yakin neman zaben shekarar 2027 ya fara gudana a fadin kasar nan, bisa jadawali da ka’idojin da hukumar zabe mai zaman kanta ta Nijeriya (INEC) ta tsara.
Aliyu ya ce kwamitin yakin neman zaben ya ga ya dace ya kai wa Sarkin Musulmi ziyara tun da wuri saboda matsayinsa na jagoran ruhaniya na al’ummar Musulmi da kuma irin gudunmawar da ya dade yana bayarwa wajen samar da zaman lafiya da hadin kan kasa.
Sauran mambobin tawagar sun hada da Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris; Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal; Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko; Sanata Adamu Aliero; Sanata Ali Modu Sheriff; tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Masari; da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da sauran manyan jami’an jam’iyyar.
