Home Lafiya Ku gaggauta rajista da mu-NAFDAC-ta fada wa masu maganin gargajiya

Ku gaggauta rajista da mu-NAFDAC-ta fada wa masu maganin gargajiya

66
0

Ku gaggauta yin rajistar hajarku wajenmu- NAFDAC ta fada wa masu magungunan gargajiya.

Abdullahi Garba Jani

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta yi kira ga masu sana’ar magungunan gargajiya da su yi rajista da hukumar don kauce wa sayar da magunguna masu hatsari ga al’umma.

Shugaban hukumar na jihar Gombe Gonzuk Nyor ne ya yi wannan kiran a lokacin da ya ke ganawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Gombe.

Mr Nyor ya ce sayar da magungunan ba tare da an yi rajista da NAFDAC ba zai zama babban laifi ganin yadda zai zama hatsari ga lafiyar al’umma.

Ya shawarce su da su zo da magungunan don yin bincike a dakunan gwaje-gwaje domin tantance sahihancin amfaninsu.

Ya ci gaba yana cewa muddin aka yi rajistar magani, to kuwa mutane za su rika sayensa ba tare da wani haufi ba.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply