Home Labarai Ku guji cin abinci mai maiko – NAFDAC

Ku guji cin abinci mai maiko – NAFDAC

157
0

Hukumar da ke kula da ingancin abinci ta Nijeriya NAFDAC ta ce tuni ta fara gudanar da wani shiri na wayar da kan al’umma game da illar da abinci mai maiko ke yi ga lafiyarsu.

Wani hasashe ya nuna cewa nau’in abinci mai maiko na halaka kimanin mutane dubu dari biyar duk shekara a fadin kasar nan.

Sannan irin wadannan nau’ika na abinci na haifar da cututtuka kamar su ciwon zuciya, cutar kwakwalwa.

Hukumar ta bukaci ‘yan Nijeriya da su sanya ido sosai wajen kula da irin wadannan nau’ika na abinci domin yin hakan zai taimaka wa hukumar.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply