Home Labarai Ku guji fallasa sirrin gwamnati – Akanta Janar

Ku guji fallasa sirrin gwamnati – Akanta Janar

112
0

Babban akanta janar na Nijeriya Malam Ahmed Idris ya gargadi ma’aikatu hadi da hukumomin gwamnati da su kaurace wa karya dokoki wajen kashe kudaden gwamnati.

Ahmed Idris ya bayyana haka ne lokacin wani taro da ya gudana tsakaninshi da manyan daraktoci da shugabannin da ke kula da sashen binciken kudade na ma’aikatu da ma hukumomin gwamnati da ya gudana ta hanyar sadarwar zamani a Abuja.

Ya bayyana rashin jin dadinsa kan yadda mafi yawan ma’aikatu da ma hukumomin ke yin baya-baya wajen adana manyan mahimman bayanai.

Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
Ziyarci shafin Facebook na DCL Hausa
 

Leave a Reply